Yadda Za A Bunkasa Fasahar Zamani Domin Samar Da Ayyukan Yi

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Yadda Za A Bunkasa Fasahar Zamani Domin Samar Da Ayyukan Yi
Jan 03, 2022
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

Send us a text

Rashin aikin yi a tsakanin matasa a Najeriya na cikin matsalolin da suka yi wa kasar katutu, har ta kai duk gwamnatin da ta zo sai an koka da gazawarta wurin samar wa ‘yan kasa abin yi.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na kunshe da bayanan yadda za a bunkasa fasahar zamani ta intanet domin samar wa ‘yan kasar aikin yi cikin sauki.