Bayanin rage adadin kwanakin zuwa makaranta da Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar a wannan zango ya dauki hankalin malaman makarantu da masana harkar ilimi a Jihar.
Malaman Makaranta na ganin cewa tsarin da zai tilastawa makarantu hutun kwana 3 a sati zai kara takure su wurin shirya jadawalin darussan da za su koyar.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na kunshe da tattaunawa ta musamman da Malamai da masana harkokin ilimi akan wannan batu.