Rufe Twitter: Yadda ’Yan Najeriya Suka Yi Asara, Gwamnati Ta Ci Riba
Najeriya a Yau
More Info
Najeriya a Yau
Rufe Twitter: Yadda ’Yan Najeriya Suka Yi Asara, Gwamnati Ta Ci Riba
Jan 14, 2022
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

A kwana akalla 220 da gwamnatin Nejeriya ta rufe harkokin kafar sada zumunta ta Twitter, ‘yan kasar sun tafka asarar makudan kudade, a yayin da gwamantin kasar kuma ta ci gagarumar riba a sakamakon matakin da ta dauka.

Masana sun yi bayanin irin makudan kudaden da Gwamnatin Tarayya za ta rika samu daga harajin da za ta rika karba daga hannun kamfanin Twitter a sakamakon amfanin da ’yan Najeriya suke yi da kafarsa, wurin gudanar da harokinsu na  kasuwanci da kuma sadar da zumunta.