Bayyana aniyar takarar shugabancin kasar da Bola Ahmed Tinubu yayi a fadar shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ta tada kura a fagen siyasar kasar.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya zaƙulo dalilanda Tinubu ya ƙaddamar da maganar takaransa a fadar shugaban ƙasar Najeriya da kuma matsayar Ƙungiyar Dattawan Arewa dangane da wanda suke son yayi takara.