Yadda Tsaro Da Tattalin Arziki Za Su Shafi Zaben 2023

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Yadda Tsaro Da Tattalin Arziki Za Su Shafi Zaben 2023
Jan 21, 2022
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

Send us a text

Yanayin tsaro da tattalin arziki na taka muhimmiyar rawa a wurin gudanar da zabe wanda kuma babban jigone wajen tabbatar da dorewar tsarin Dimokuradiyya.

Taron tattaunawa na shekara-shekara da kamfanin Media Trust mai buga jaridar Daily Trust na wannan karon ya mayar da hankali ne a kan rawar da yanayin tsaro da tattalin arzikin Najeriya za su taka wurin juya akalar zaben kasar na shekarar 2023.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattaro bayanan masana akan harkokin tsaro, tattalin arziki da tsaro.