Da Bazar Wa Za A Yi Rawa A Sabuwar Tafiyar TNM?

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Da Bazar Wa Za A Yi Rawa A Sabuwar Tafiyar TNM?
Feb 24, 2022
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

Send us a text

Yayin da zabukan 2023 ke kara karatowa, fagen siyasar Najeriya sai kara tumbatsa yake yi.

Tuni ‘yan siyasa suka fara kai-kawo don fasalta bukatunsu da hanyoyin cimma buri.

A wannan yanayi ne wasu gaggawa ‘yan siyasa, ciki har da tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso suka kudiri aniyar wata sabuwar tafiya.

Sai dai wasu na ganin ba a fage horar wannan tafiya a ka lokaci ba, yayin da wasu ke ganin don biyan boyayyiyar bukatar wani ko wasu za a yi ta

Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari a kan hakikanin inda aka dosa da guzirin da aka tanada da ma tsara bar da za a dawo da ita.