Me Ya Sa ’Yan Najeriya Suka Fara Yanke Kauna Da Samun Sa’ida?

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Me Ya Sa ’Yan Najeriya Suka Fara Yanke Kauna Da Samun Sa’ida?
Oct 11, 2024
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Muhawara ta barke a Najeriya bayan sanar da aka sanar da karin farashin man fetur a gidan gidajen mai na NNPC a kan wane ne zai kare muradun ’yan kasa, ya hana a yi musu hawan kawara?

’Yan kasa da dama dai na ganin wannan kari a matsayin wani karin mataki na takura wa rayuwarsu, wadda tuni dama take cikin wani yanayi na tsaka-mai-wuya.