Daya daga cikin nau’ukan harajin da gwamnatoci suke karba shi ne harajin VAT wanda akan dora a kan kayayyaki ko hidimomi.
Tasirin wannan haraji a kan farashin kayayyaki ya sa gwanatin Najeriya dauke harajin a kan wasu kayan abinci.
Amma bayan watanni da daukar wannan mataki, ’yan Najeriya ba su ga tasirin yin hakan ba.
Shirin Najeriya A Yau zai bincika dalilan da suka sa hakan.