Fashewar Tankar Mai: Asarar Da Al’ummar Majiya Suka Tafka

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Fashewar Tankar Mai: Asarar Da Al’ummar Majiya Suka Tafka
Oct 18, 2024
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Galibin waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon fashewar tankar man da ta yi ajalin sama da mutum 150 a garin Majiya na Jihar Jigawa matasa ne.

Ɗaya daga cikinsu, Hassan Hamza, matashi ne da ya yi karatu a fannin Harhaɗa Magunguna, karatun da ake matuƙar buƙatar masu yinsa a tsakanin al’umma.

A shirin Najeriya a Yau na lokacin za mu yi nazari ne a kan girman asarar da al'ummar Jami’ar Jihar Jigawa ta tafka.