“Matsin Tattalin Arziki Ya Sa Ba Na Iya Aikina Yadda Ya Kamata”

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
“Matsin Tattalin Arziki Ya Sa Ba Na Iya Aikina Yadda Ya Kamata”
Oct 31, 2024
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Alamu sun nuna cewa sakamakon kuncin rayuwa da ake fama da shi a Najeriya, ingnacin aikin da ma’aikata suke yi yana raguwa.

Aiki yana ingnatuwa ne dai da samun wasu abubuwa da suka hada da kyakkyawan yanayin wurin aiki da isasshen hutu da kwanciyar hankali da kuma biyan bukatar ma’aikaci a dukkan lokaci.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai tattauna ne kan yadda matsin tattalin arziki ke shafar ayyukan ma’aikata da ma masu aikin hannu a Najeriya.