Abin Da Ya Kamata A Yi Da Kananan Yara Masu Zanga-Zanga

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Abin Da Ya Kamata A Yi Da Kananan Yara Masu Zanga-Zanga
Nov 04, 2024
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Gurfanar da yaran nan da aka kama watanni uku da suka gabata yayin zanga-zangar ‘#EndBadGovernance’ na ci gaba da yamutsa hazo a Najeriya.

Mutane da dama dai, musamman a Arewa, suna ta tofin Allah-tsine a kan kamen yaran, wadanda wasu suke cewa kanana ne, shekarunsu ba su kai a kama su ba ballantana a kai su gaban kotu.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai tattauna ne kan tanadin doka game da kamen kananan yara, da kulle su, da kuma gurfanar da su gaban kuliya.