Shin Addu’oi Kadai Najeriya Take Bukata Don Ficewa Daga Matsaloli?

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Shin Addu’oi Kadai Najeriya Take Bukata Don Ficewa Daga Matsaloli?
Nov 05, 2024
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Galibin ’yan Najeriya dai sun yarda cewa Allah ne mai bayarwa, Shi ne kuma mai hanawa.

Mai yiwuwa hakan ne kan sa a rika yin kira, musamman ga mabiya addianai mafiya rinjaye na Musulunci da Kiristanci, da su  yi addu’oi don samun waraka daga matsalolin da aka fama da su.

Sai dai kuma wasu ’yan kasa suna ganin fadar haka alama ce da take nuna cewa siukuwa ta kare saura zamiya.

Shirin Najeriya A Yau zai yi Nazari ne kan wannan batu.