Yadda Za A Kauce Wa Gadon Ciwon Suga

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Yadda Za A Kauce Wa Gadon Ciwon Suga
Nov 14, 2024
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa akalla ’yan Najeriya miliyan biyar ne suke cikin hadarin kamuwa da ciwon suga nan da shekarar 2030.

Yaduwar lalurar a tsakanin wadanda iyayensu suke fama da ita tana cikin hanyoyin da suke taimakawa wajen karuwar ta. 

Albarkacin Ranar Ciwon Suga ta Duniya, shirin Najeriya A Yau zai tattauna a kan hanyoyin da wadanda suke fuskantar barazanar kamuwa da lalurar za su bi don kauce mata.