Kalubalen DaZai Yi Wa Zababben Gwamnan Jihar Ondo Dabaibayi

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Kalubalen DaZai Yi Wa Zababben Gwamnan Jihar Ondo Dabaibayi
Nov 18, 2024
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us Fan Mail

Tun bayan da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ayyana Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe Zaben Gwamna da aka gudanar a Jihar Ondo ranar 16 ga watan Nuwamba, hankula suka karkata zuwa ga kalubalen da ke gabansa.

Kama daga rikicin cikin gida a jam’iyyarsa ta APC zuwa ga barazanar jam’iyyun adqawa da muradun al’ummar da ya yiwa alkawura, anya Aiyedatiwa bai sha ta fi cikinsa ba kuwa?

Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari a kan abubuwan da Zababben Gwamnan na Jihar Ondo ka iya fuskanta bayan ya sha rantsuwar kama aiki.