Abin Da Ya Sa Mutanen Tudun Biri Suka Juya Baya Ga ₦33B

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Abin Da Ya Sa Mutanen Tudun Biri Suka Juya Baya Ga ₦33B
Nov 26, 2024
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Al’ummar Tudun Biri sun ce su da ma ba su sa a ka bayan da aka ba da labarin cewa kotu ta yi fatali da wata kara da aka shigar a madadin su.

Tun a bara dai, lokacin da wasu lauyoyi suka shigar da ƙara suna neman a bi wa wadanda wani harin rundunar sojin sama a kan kauyen ya hallaka hakkinsu, mazauna yankin da dama suka nesanta kansu da lamarin.

Shirin Najeriya a Yau na wannan lokacin zai duba dalilinsu na sa ƙafa su shure wannan kuɗi.