Duk wanda ya shekara arbain zuwa sama ya san irin tarbiyyan da ya samo daga wurin iyayen sa a da baya can, irin mu’amalan dake tsakanin sa da iyaye har ma da shakuwan dake tsakanin ‘ya’ya da iyaye.
A yanzu kuwa abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincabe sukayi wa iyaye yawa.
Daya daga cikin manyan sauyin da aka samu sun hada da aikin gwamnati ko aikin wata da iyaye mata suke yi a wannan zamani wanda hakan a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawan da ‘ya’ya suke samu.
Shirin Najeriya A Yau zai yi Nazari ne kan irin kalubalen da iyaye ke fuskanta a wannan zamani wajen tarbiyyan ‘ya’yan su.