Wani rahoto da Kungiyar Likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta fitar ya nuna cewa Arewa maso Yamma ta fi kowacce shiyya yawan karuwar yara masu tamowa.
A shiyyar kuma, inji rahoton, Katsina ta fi ko wacce jiha yawan masu fama da cutar.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi bincike ne don gano yadda lamarin yake.