Yadda Direbobi Suke Zaman Kashe Wando A Tasha

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Yadda Direbobi Suke Zaman Kashe Wando A Tasha
Dec 20, 2024
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

A shekarun baya, idan mutum ya shiga tashoshin mota a biranen Najeriya a irin wannan lokaci, zai same su cike da jama’a da hayaniya.

Sai dai a bana, a tashoshi da dama, wasu direbobin a kwance suke yayin da fasinjoji suke zaune tsawon sa’o’i suna jiran tsammanin motoci su cika.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan faruwar hakan a karshen wannan shekarar.