Abin Da Ya Sa ’Yan Sanda Suke Kama Mutanen Da Ba Su Ji Ba, Ba Su Gani Ba

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Abin Da Ya Sa ’Yan Sanda Suke Kama Mutanen Da Ba Su Ji Ba, Ba Su Gani Ba
Dec 24, 2024
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Lokacin bukukuwa lokaci ne da ake samun karuwar zirga-zirga da hada-hadar jama’a.

Wannan ne ya sa hukumomin da nauyin samar da tsaro ya rataya a wuyansu suke kara kaimi wajen ganin sun tabbatar da doka da oda.

Sai dai  wasu ’yan Najeriya sukan yi zargin cewa ’yan sanda kan yi amfani da wannan dama don kamen mutane babu gaira babu dalili.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai yi duba ne kan sahihancin wannan zargi.