Ranar 26 ga watan disambar duk shekara ne ake rabon kyaututtuka a cigaba da gudanar da bukuwan kirsimeti wanda ake ma wannan rana da boxing day.
Alumma da dama da sunji boxing day abun dake fara zuwa musu a rai shine wasan dambe da ake yi a wasu kasashe da ake kira da boxing.
Shirin Najeriya A Yau zai yi duba ne kan wannan rana na Boxing Day don warware zare da abawa.