Saye ko sayar da guraben aiki wani abu ne da yake karuwa kuma yake barazana ga ci-gaban al’umma a Najeriya.
Akan yi zargin cewa mutane suna bin wasu hanyoyin da ba su dace ba kafin a ba su aiki a gwamnati.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wadannan hanyoyi da illar da suke haifar wa al’umma da kuma dabarun kawo karshensu.