Yadda Rashin Ɗaukar Darasi Ya Haddasa Gagarumin Asara A Suleja

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Yadda Rashin Ɗaukar Darasi Ya Haddasa Gagarumin Asara A Suleja
Jan 20, 2025

Send us a text

Ƙiyasi ya nuna cewa an yi asarar miliyoyin Naira bayan da shaguna makare da kayayyaki da motocin hawa da na haya suka ƙone ƙurmus, uwa uba kuma rayuka aƙalla 80 suka salwanta sakamakon fashewar tankar mai a Marabar Dikko da ke kusa Suleja a Jihar Neja.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da faɗuwar tanka  ta haddasa asarar dukiya da rayukan mutane masu yawa. 
Ko me ya sa ya sa har yanzu ’yan Najeriya ba su shiga taitayin su ba da zuwa diban man fetur idan tanka ta fadi?

Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokacin zai tattauna a kai.