Yanzu haka, saura mako biyu wa’adin da aka deba wa maniyyata Hajjin bana su biya kudin kujerar ya cika, amma rahotanni daga wasu sassan kasar nan na nuna cewa kalilan ne suka iya biyan.
Kudin kujerar hajjin ya tsorata ’yan Najeriya a bana, bayan da hukumomi suka ce duk mai sha’awar sauke farali sai ya biya zunzuruntun kudi sama da Naira miliyan takwas.
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.