Kudaden crypto na cikin hanyoyin da zamani ya zo da su da nufin sauƙaƙa hada-hada a tsakanin alumma, musamman a ƙasashen da suka ci gaba.
Sai dai a Najeriya, har yanzu ba kowa ne ya san wannan harka da kuma yadda ya kamata a yi ta ba, musamman duba da yadda kudin na crypto ya yi daraja a fadin duniya.
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokacin zai yi nazari ne a kan alfanun da ’yan Najeriya za su iya samu daga kuɗin crypto, musamman tun bayan zaɓen Donald Trump a matsayin Shugaban Ƙasar Amurka a karo na biyu.