Akan ce “Noma tushen arziki”. Mutane da dama za su iya bayar da labarin da ke tabbatar da hakan; domin kuwa ko ba komai idan mutum ya samu abinci ya ci ya koshi babban arziki ne.
Wasu ’yan Najeriya kan shuka kayan abinci a unguwannin su don sama wa kan su abincin da za su ci.
Sai dai masana na ganin da wadannan mutane za su inganta wannan noma da sun sama wa kansu kudaden shiga.
Shirin Najeriya aYau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan hanyoyin da ’yan Najeriya za su iya bi don sama wa kansu kudaden shiga bayan sun noma abin da za su ci.