Dalilan Da Suka Sa Zamu Kashe Naira Biliyan Biyu Da Rabi Kan Auratayya A Kano

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Dalilan Da Suka Sa Zamu Kashe Naira Biliyan Biyu Da Rabi Kan Auratayya A Kano
Feb 03, 2025
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us Fan Mail

Tun bayan da jihar kano ta fitar da rahoton ware zunzurutun kudi har naira biliyan biyu da rabi don auratar da marasa aure a jihar ne dai batun ke ta shan suka daga bangarori daban daban a fadin Najeriya.


Wasu na ganin jihar na da wasu bukatun da suka fi auratar da alumma muhimmanci da ya kamata ace gwamnatin ta mayar da hankali a kai.


Shirin Najeriya A Yau na wannan rana yayi nazari ne kan dalilan da suka sa jihar Kano ta ware Naira Biliyan Biyu da rabi don aurar da ‘yan mata da zawarawa.