A tsakanin Hausawa akan yi wa jaririya wani nau’i na kaciyar mata, wanda ake kira yankan angurya, kwana bakwai da haihuwarta.
Ko menene alfanu ko illar wannan al’ada ga ’ya’ya mata?
Albarkacin Ranar Yaki da Kaciyar Mata ta Duniya, shirin Najeriya A Yau zai yi nazari a kan wannan al’ada da tasirinta a rayuwar mata.