Shin mene ne dalilin faɗuwar farashin tumatir warwar a kasuwa?
Idan ba a manta ba, a watannin baya farashin Tumatur yayi tashin gwauron zabo wanda aka dade ba’a ga irin sa ba.
A wancan lokacin, sai da farashin tumaturin ya kai ga iyalai da dama sun hakura dashi sun koma sayen na gwangwani ko na leda.
Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai yi nazari a kai.