Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya?

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya?
Feb 10, 2025
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

A tsakanin al’umma akan karkasa mutane gida-gida a bisa mizani na tattalin arziki, musamman a tsarin jari-hujja: akwai mawadata, akwai matalauta.
A tsakanin al’umma akwai aji na mutane masu matsakaicin samu wanda ake kira “Middle Class”.


Akan saka mutane a wannan aji ne galibi bisa la’akari da aiki ko sana’ar da suke yi, da kudin da suke samu, da matakin ilimin da suka kai, da ma matsayinsu a tsakanin al’umma.
Sai dai a baya-bayan nan irin wadannan muntane sun bi sahun matalauta wajen korafi game da yadda suke dandana kudarsu saboda tsadar rayuwa.


Shin a iay cewa har yanzu akwai wannan aji na mutane a Najeriya ke nan?
Wannan ne batun da shirin Najeriya  a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.