Bayanai daga sassa daban-daban na Najeriya suna nuni da cewa farashin kyayyakin masarufi na ta faduwa a kasuwanni.
Kafin hakan dai farashin ya yi ta tashi, har ya kai ga duk abin da mutum ya saya a yau, idan ya koma kasuwa bayan kwana biyu zai ji an ce ya tashi.
Ko wadanne dalilai ne suka sa farashin kayayyakin masarufi suke ta sauka a yanzu?
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan wannan batu.