A kwanakin baya ne dai shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kirkiri sabbin hukumomin shiyyoyin kasar nan da nufin kawo cigaba ga wadannan shiyyoyi.
Gabanin kirkirar wadannan hukumomin, gwamnatin da ta gabata karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ce ta fara kirkirar hukumar raya yankin Neja Delta bayan wasu kalubale da suka dabaibaye yankin.
Na baya bayan nan shine hukumar raya yankin Arewa maso tsakiyar kasar nan bayan da ‘yan yankin suka cigaba da tura korafin su na maida su saniyar ware.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan irin cigaban da wadannan shiyyoyi zasu samar ga alummar kasa.