A daidai lokacin da wasu alumma ke murnar saukar farashin kayayyakin abinci a kasuwanni kamar su shinkafa, masara da sauran kayan hatsi.
Shima farashin flawa da ake amfani dashi wajen sarrafa biredi, gurasa da sauran makulashe ya sauka a kasuwa.
Sai dai duk da saukar da farashin flawar tayi, alumma na cigaba da kokawa kan yadda har yanzu basu gani a kasa ba.
Tun makonni biyu da suka gabata ne dai aka bayyana farashin flawar ta sauka a kasuwa kamar sauran kayayyakin masarufi, to amma ba kamar sauran kayan abinci ba, har yanzu ba a ga sauyi a farashin biredi ba.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa masu sarrafa biredi suka ki sauke farsashin biredi duk da karyewar farashin fulawa a Kasuwa.