Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri
Feb 24, 2025
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Cutar kyandar biri da aka fi sani da Mpox ta kara bulla a Najeriya.
Na baya bayan nan shine wanda ta bulla a jihar Filato inda aka samu wadanda suka kamu da ita mutum 11 da sai wanda ya rasa ransa mutum daya.


Cutar ta kyandar biri ta bulla ne a kananan hukumomi biyar da suka hada da Jos ta Arewa, Bokkos, Shendam, Mangu da kuma Kenke.


Ko wadanne irin matakai ya kamata alumma su dauka don kaucewa kamuwa da wannan cuta?
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi Nazari ne kan matakan kariya daga cutar kyandar biri.