Wutan lantarki a Najeriya ya zama ginshikin rayuwa da alumma basa iya rayuwa ba tare dashi ba.
A duk lokacin da aka ce an dauke shi zaka ga yadda alumma kan shiga cikin matsanancin hali, wasu da dama sun ta’allaka ne dashi wajen tafiyar da harkokin su na yau da kullum, kai har ma da kasuwanci.
A kwanakin baya ne jihohin Kaduna, Sakkwato, Zamafara da kuma jihar Kebbi suka fuskanci daukewar wutar lantarki na tsawon wasu kwanaki inda hakan ya jefa alummar wadannan jihohi cikin halin ni ‘ya su.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi Nazari ne kan halin da alummar dake karkashin kamfanin rarraba wuta na Kaduna electric zasu shiga in ma’aikatan ta suka shiga yajin aiki.