Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar Da ‘Ramadan Basket’ Ba

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar Da ‘Ramadan Basket’ Ba
Mar 04, 2025
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

A aladance, a duk lokacin da aka ce watan Ramadana ya karato samari da ‘yan mata kan yi musayar kyaututtuka don kyautata wa abokan zaman su.

Misali, a lokacin azumi samari kan sayi kayan bude baki da suka hada da madara, kwai, da sauran kayan makulashe wanda ake yiwa lakabi da ‘’Ramadan Basket’’ a turance don kaiwa ‘yan matan su.

Sai dai a wannan shekarar da alamun abun ya sauya salo, domin kuwa ba kamar yadda aka saba ba, kafafen sada zumunta basu baza hotuna da faya fayen bidiyon wadannan Ramadan Basket din ba.

Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi duba ne kan dalilan da suka hana samari bada ‘’Ramadan Basket’’ wannan shekarar.