Fiye da wata guda ke nan tun bayan da Matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 890 zuwa naira 825 kowace lita.
Bayan wannan ragi ne dai shi ma Kamafanin Mai na Kasa wato NNPCL ya sanar da rage nasa farashin.
Sai dai har yanzu ba a ga ragin a gidajen mai ba.
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan lamari.