Hadisi ya tabbatar da yadda cin abinci tare yake kara dankon zumunci da kaunar juna da albarka a tsakanin al’umma.
Mai yiwuwa wannan ne ya sa akan samu Karin kusanci da shakuwa a tsakanin duk iyalan da kan zauna su ci abinci.
Ko kafin watan azumi dai, wasu magidantan kan mayar da cin abinci tare da tare da iyalin su al’ada.
Shin ko mene ne matsayin bude-baki tare da iyali a watan Ramadana?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin alfanun da bude baki tare da iyali yake da shi.