Watan azumi lokaci ne da akan samu wasu ma’aikatu sun sassauta wa ma’aikata ta hanyar yi musu rangwame kamar rage musu yawan sa’o’in aiki.
Sai dai a lokacin da wadannan mutane suke samun rangwame, akwai wadanda suke ayyuka ko sana’o’in da suka dogara da su ciyar da iyalansu.
Sau da dama irin wadannan mutane sai sun fita sun yi aiki a rana, duk da suna azumi, suke samun abin da za sus aka a bakin salati.
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin ladan da masu aikin karfi suke samu yayin da suke azumi.