Abubuwan Da Suke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Abubuwan Da Suke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya
Mar 11, 2025
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da daukar dumi  yayin da ’yan kasa da dama suka yi kasake suna jiran girgiza ta gaba wadda wasu suke ganin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya diga mata dan ba.


A baya-bayan nan dai an yi ta tsegunguma da rade-radi a kana bin da wasu jiga-jigan ’yan siyasar kasar nan, musamman ’yan adawa da ’ya’yan jam’iyya mai mulki wadanda suke takun saka da Shuaban Kasa Bola Ahmed Tinubu suke kullawa.
Yanzu ta fara wari, an ji Malam Nasiru ya bayar da sanarwar ficewarsa daga jam’iyyar APC da tsallakawa zuwa SDP.


Shin ko me zai biyo bayan wannan girgiza da tsallen badaken Malam Nasiru da dirarsa suka haifar?
Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai duba.