Ko Yarjejeniya Da ’Yan Ta’adda Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Arewa?

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Ko Yarjejeniya Da ’Yan Ta’adda Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Arewa?
Mar 13, 2025
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Masu iya magana kan ce dole uwar na ki. Matsalar tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa musamman a Arewacin Najeriya tana tilasta wa wasu al’ummomi zakulo hanyoyin samun sa’ida ko yaya suke.


Daya daga cikin wadannan hanyoyi da wasu al’ummomi suka runguma ita ce kulla yarjejeniya da ’yan bindigar dake addabar yankunansu.
Shin ko cimma yarjejeniya da ’yan fashin daji mafita ce daga matsalar tsaro?
Wane hali yankunan da suka kulla irin wannan yarjejeniya suke ciki a halin yanzu?


Shirin Najeriya a Yau na wannan ;pkaci zai yi duba ne kan yarjejeniyoyin da wasu al’ummomi suke kullawa da ’yan ta’adda a Arewacin Najeriya.