Lokutan sallah kamar yadda aka sani lokacin ne na farin ciki, nuna godiya ga niāimar da Allah yayi mana da kuma bauta.
Kazalika lokacin ne da zamu lura da tabbatar da aiyukan da zamu aikata su zama ingattattu.
Ko wadanne irin abubuwa ne mutane ya kamata su aikata kafin da kuma ranar sallah?
Wadanne hanyoyi za a bi don tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da bikin sallah?
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi Nazari ne kan abubuwan da musulmi ya kamata suyi gabani da kuma ranar sallah.