A Najeriya ana tafka muhawara a kan yadda farashin danyen man fetur yake kara faduwa a kasuwannin duniya.
Wannan lamari dai ya haddasa damuwa a zukatan wasu ’yan Najeriya, kama daga masana tattalin arziki zuwa ga jami’an gwamnati, kasancewar danyen mai ne mafi muhimmanci a cikin hanyoyin samun kudin shiga.
Sai dai tambayar da wasu ’yan kasa suke yi ita ce: shin yaya wannan faduwa ta farashin danyen mai za ta shafi rayuwar talakan Najeriya?