Tun zamanin kaka da kakanni ake gudanar da kananan sana’oi, wanda alumma ke dogaro dasu don biyan bukatun su na yau da kullum.
Irin wadannan sana’oi sun hada da saka, jima, balangu, suyan kosai ko masa da dai sauran sana’oi da alumma keyi.
A da can baya irin masu wadannan sana’a sun dogara ne da masu wucewa a bakin hanya don siyar da abun da suke sana’antawa ko kuma wadanda suka samu a yayin da suka dauki tallan sana’ar tasu.
Sai dai a wannan zamani irin masu wannan sana’aoi na fuskantar barazana daga wurin ‘yan zamani ‘yan bana bakwai da suka shigar da zamani ciki suke neman kwace wannan sana’a daga iyaye da kakanni ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta wajen tallata sana’oin su.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai tattauna ne kan hanyoyin da mutane zasu habbaka sana’oin su ta hanyar amfani da kafafen sada zumuntar zamani.