Zazzabin cizon sauro, wato malaria, na cikin cututtuka mafiya shahara da kuma hadari a Najeriya. Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya nuna cewa Najeriya na da kaso mafi girma na mace-macen da cutar take haifarwa a duniya.
Sau da yawa wanda ya kamu da cutar ta malaria kan sake kamuwa da ita bayan ya warke.
Ko me ya sa magungunan zazzabin cizon sauro suka daina aiki a jikin mutane?
Wannan batu shirin Najeriya A Yau zai duba yayin da ake bikin Ranar Malaria ta Duniya.