Yadda Naira Biliyan Daya Ta Salwanta A Gobarar Kasuwar Jos

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Yadda Naira Biliyan Daya Ta Salwanta A Gobarar Kasuwar Jos
May 02, 2025
Idris Daiyab Bature

Send us a text

Kusan Naira biliyan day ace aka kiyasta ta salwanta sakamakon gobarar da ta kone wane sashe na babbar kasuwar dake tsakiyar Jos babbar birnin jihar Filato.


An rawaito cewar gobarar ta lakume shaguna fiye da dari biyar, galibinsu na masu sayar da kayan gwanjo.
Mutane da dama dai sun rasa hanyar cin abincinsu, kasancewar galibinsu sun sun dogara ne da samun da suke yi a kullum a wannan kasuwa don ciyar da iyalansu.
Ko wanne hali wadanda suka tafka wannan asara suke ciki bayan wannan ibtilai?


Wannan na cikin batutuwan da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba.