A ko’ina a Nahiyar Afirka za a iya samun ɗan Najeriya da ya bar ƙasar sa domin rayuwa a wata ƙasa.
A yau ba sai an je Turai ko Amurka ba – kasashe irin su Mali, Ghana, Libya, Sudan da sauran su suna cike da matasa ’yan Najeriya wadanda suka je ci-rani.
Shin me ya sa wadannan matasa suke barin Najeriya – uwa ga Afirka, mai albarkatu da dama?
Me suke samu a waje da ba za su iya samu a gida Najeriya ba?
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai duba.