Yin gwagwarmaya ko fafutuka wani abu ne da ke cikin jinin dan Adam, musamman idan yana kokarin ganin an samu sauyi ko cigaba a al'umma.
Sai dai a Najeriya, sau da yawa ana danganta kalmar "gwagwarmaya" da rikici ko sabani da gwamnati.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan yadda za a yi gwagwarmaya ba tare da an taka doka ba.