Abun Da Yasa Muka Ƙasa Kawo Karshen Tamowa A Wasu Jihohin Arewa Maso Gabas

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Abun Da Yasa Muka Ƙasa Kawo Karshen Tamowa A Wasu Jihohin Arewa Maso Gabas
May 09, 2025
Idris Ɗaiyab Bature

Send us a text

Hukumomi a jihar Yobe sun dora alhakin kazancewar matsalar tamowa a kan rikicin Boko Haram da rashin shayar da jarirai nonon uwa yadda ya kamata da kuma gurbacewar harkar kiwon lafiya, da sauran su.


Bayanin hakan na zuwa ne bayan ambato Babban Jami’i mai Kula da Ayyukan Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mista Mohamed Malick Fall, yana  yara miliyaan daya a jihohin Borno da Adamawa da Yobe suna fuskantar barazanar rasa rayukansu sakamakon cutar tamowa a bana.
An kuma ruwaito shi yana cewa wannan adadi ya rubanya na yaran da suka fuskanci barzanar a bara.


Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan hanyoyin da za abi don magance Tamowa a wasu jihohin Arewa maso Gabas.