Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta yi amai ta lashe.
Bayan ta musanta dukkan zarge-zargen da aka yi cewa tana da hannu a rashin kyawun sakamakon jarrabawar da ta shirya, Shugabanta ya fito ya amsa laifi.
Yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai, Farfesa Is-haq Oloyede ya ce dalibai 379,997 abin ya shafa, kuma hukumar zata sake shirya musu wata jarabawar.
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan dalilan Hukumar ta JAMB.