Jam’iyyar NNPP wadda Dr. Boniface Aniebonam ya kafa a shekarar 2001, ta samu karfi sosai a Jihar Kano bayan tsohon gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga cikinta a shekarar 2022 tare da mabiyansa na Kwankwasiyya.
Shigowarsa ta farfado da jam’iyyar, inda ta samu gagarumar nasara a zaɓen 2023 ta hanyar lashe kujerar gwamna da wasu kujerun majalisa.
Sai dai rikicin cikin gida da rikice-rikicen shugabanci suna ma jamiyyar rauni wanda hakan ya haddasa ficewar wasu manyan ‘ya’yanta zuwa APC, lamarin da ke haifar da tambaya kan makomar NNPP a Kano.
Shin jam’iyyar NNPP za ta kai labari a Kano, musamman bayan ficewar wasu daga cikin jiga-jiganta?
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba.